ABNA24: ministan cikin gida Hasham Almashishi ya kafa sabuwar gwamnati. Tashar radiyo
ta FM Tunis ta bada sanarwa a safiyar yau Lahadi kan cewa shugaba Sa’id ya
bukaci Almashisi ya kafa hukuma a cikin kwanaki 30 masu zuwa. Almashishi dais
hi ne mutun na hudu wadanda aka bukace shi ya kafa gwamnati tun bayan borin da
ya kifar da gwamnatin zainul-Abadin abin Ali. Amma idan har ya kasa samun
amincewar ‘yan majalisar dokokin kasar 109 cikin 217 to shugaban kasa yana da
damar kiran sabon zaben majalisar dokokin kasar.
Tsohon firai ministan kasar Elyas Fakhfakh ya sauka daga mukaminsa bayan da ya sami sabani da babbar jam’iyyar kasar wato Jam’iyyar Annahdha bayan watanni kadan da kafa gwamnati.
342/